Skip to main content

An yi garkuwa da yan ƙasar Italiya uku da wani ɗan Togo a Mali

Rahoto kai-tsaye

  1. SHAREDAn yi garkuwa da yan ƙasar Italiya uku da wani ɗan Togo a Mali

    /..

    Rahotanni daga ƙasar Mali na cewa an yi garkuwa da ƴan ƙasar Italiya uku da wani mutum guda dan ƙasar Togo.

    An bayyana cewa wasu ƴan bindiga ne suka yi garkuwa da su a kudu maso gabashin ƙasar. Jami'an tsaro a ƙasar sun ce ana kyautata zaton mutanen masu bin ɗariƙar Jehovah's Witnesses ne.

    An sace su ne daga wata mota a ranar Alhamis a lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa yankin Koutiala.

    Cikin waɗanda ake zargin an sace har da wani yaro.

    An shafe shekara da shekaru ana fuskantar rikici na masu iƙirarin jihadi a Mali inda kuma aka shafe shekaru ɓarayi da ƴan tawaye na cin karensu ba babbaka.

    Babu sanarwa a hukumance dangane da wannan lamarin daga gwamnatin ta Mali.

  2. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo karshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan irin labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a kai.

  3. Dakarun Tigray a Habasha za su saki fursunonin yaƙi sama da 4,000

    Dakarun da ke kula da yankin Tigray a Habasha sun bayyana cewa za su saki fursunonin yaƙi 4,206 ciki har da mata 401.

    Dakarun sun ce wasu daga cikin matan ma sun haihu yayin da suke a tsare.

    Wata sanarwa da ofishin harkokin waje na yankin Tigray ya fitar ya bayyana cewa matakin ya zo ne bayan shiga tsakani da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi a karkashin Kungiyar Tarayyar Afrika inda yake kokarin kawo karshen yakin da aka shafe wata 19 ana yi.

    Akasarin wadanda za a saki an kama su ne a yayin da ake yaki a wajen iyakar Tigray kuma sojojin da aka ɗauka ne.

  4. Dala miliyan 4.7 sun yi ɓatan-dabo a Malawi

    ..

    Wani bincike da aka gudanar game da yadda aka kashe kudin tallafin korona a Malawi ya gano cewa kusan $4.7m sun yi batan-dabo daga cikin $21m da aka ware domin kawo karshen zagaye na biyu na annobar ta korona.

    Wannan kudin daban yake da $881m da aka ware don shawo kan zagaye na daya na annobar korona a 2020 wanda bincike ya nuna cewa an kashe su ba yadda ya kamata ba ko kuma ba a san inda suke ba.

    Bayan gudanar da bincken farko, Shugaba Lazarus Chakwera ya yi alkawarin hukunta wadanda aka samu da laifi kuma an gurfanar da mutane da dama a kotu, ko da yake har yanzu babu wanda aka kammala yi wa shari'a.

    Bincike na baya-bayan nan - mai shafi 66 da Akanta Janar na kasar ya gudanar - ya bayyana cewa an aikata ba daidai ba, da suka hada da rashin kai magungunan cutar, biyan alawus-alwus ga ma'aikatan-bogi da kuma sayen fetur ba tare da an rubuta hakan a littafi ba.

  5. Ƙasashen ƙungiyar G7 za su ƙara ba Ukraine Tallafi

    Ministocin kudin kungiyar kasashe 7 masu kafin tattalin arziki a duniya wato G7, sun amince da karin tallafin kudi na dala biliyan 9 da miliyan dari biyar ga Ukraine, abin da ya kawo adadin tallafin kawo yanzu ya kai kusan dala biliyan 20.

    Bayan kammala taron da suka yi a Jamus, ministocin sun ce wannan tallafi zai taimakawa gwamnatin Ukraine ci gaba da samar da abubuwan da take bukata a kasar a yayin da har yanzu Rasha ke ci gaba da kai wa Ukraine hare-hare.

    Hare-haren sun matukar shafar harkokin karbar haraji, sannan kuma kasar a kowanne wata tana bukatar kusan dala biliyan 5 domin biyan ma'aikatan gwamnati kudadensu.

    Ministocin na G7, sun kuma sha alwashin ci gaba da tsaya wa Ukraine tare da tabbatar da cewa a shriye suke su kara bai wa kasar tallafin da take bukata.

  6. IMF zai ba sabuwar gwamnatin Somalia sama da dala miliyan 400

    ..

    Asusun bayar da lamuni na duniya IMF, ya tabbatar da cewa sakamakon jan kafar da aka yi a zaben sabon shugaban kasa a Somalia makon daya wuce, asusun a yanzu zai mika fiye da dala miliyan 400 ga gwamnatin kasar.

    Kudin na da matukar muhimmanci saboda za a biya ma’aikatan gwamnati da sojojin kasar albashi.

    Sabon shugaban kasar, Hassan Sheikh Mohamud, ya ce yana tuntubar sabuwar gwamnatin a kan sabbin tsare-tsaren bunkasa tattalin arzikin kasar.

    Kafin zaben, rikicin siyasar kasar ya kawar da hankalin gwamnati daga fatattakar masu ikirarin jihadi da kuma mayar da hankali a kan magance fari a kasar.

  7. $4.7m da aka ware don maganin cutar korona sun yi batan-dabo a Malawi

    An gabatar da rahoton ne ga ministan kudi domin ya dauki mataki.

    Wani bincike da aka gudanar game da yadda akas kashe kudin tallafin korona a Malawi ya gano cewa kusan $4.7m sun yi batan-dabo daga cikin $21m da aka ware domin kawo karshen zagaye na biyu na annobar ta korona.

    Wannan kudin daban yake da $881m da aka ware don shawo kan zagaye na daya na annobar korona a 2020wanda bincike ya nuna cewa an kashe su ba yadda ya kamata ba ko kuma ba a san inda suke ba.

    Bayan gudanar da bincken farko, Shugaba Lazarus Chakwera ya yi alkawarin hukunta wadanda aka samu da laifi kuma an gurfanar da mutane da dama a kotu, ko da yake har yanzu babu wanda aka kammala yi wa shari'a.

    Bincike na baya bayan nan - mai shafi 66 da Akanta Janar na kasar ya gudanar - ya bayyana cewa an aikata ba daidai ba, da suka hada da rashin kai magungunan cutar, biyan alawus-alwus ga ma'aikatan-bogi da kuma sayen fetur ba tare da an rubuta hakan a littafi ba.

    An gabatar da rahoton ne ga ministan kudi domin ya dauki mataki.

  8. An kammala kwashe fararen-hula da sojoji da suka ji rauni a Azovstal

    .

    Wani babban jami'in soja a Ukraine ya ce an kammala kwashe fararen-hula da sojojin da suka ji rauni a masana'antar karafa ta Azovstal da ke Mariupol a Ukraine.

    Deny Prokopenko ya bayyan a cikin wani sakon bidiyo cewa har yanzu ana kokari wajen ganin an ciro gawarwakin wadanda suka mutu a yayin yakin.

    Rundunar leken asirin sojin Birtaniya ta ce akwai kusan sojojin Ukraine 1700 da ba mamaki sun mika wuya a masana'antar ta Azovstal.

    Shi kuwa ministan harkokin tsaron Rasha, Sergei Shoigu, ya bayyana cewa adadin sojojin da suka mika wuyan zai iya kai wa kusan dubu biyu.

    Ya ce akwai zaman dar-dar a wasu yankuna da ke yammaci, muna kara daukar matakan kariya, a wanann yanayi jami'anmu na kara jajircewa.Sannan mun kara samar da wasu rundunoni soji don mu kai ga gaci.

  9. Rasha ta dakatar da sayarwa Finland gas

    .

    Rasha ta dakatar da sayarwa Finland gas, in ji wani kamfanin gas na kasar.

    Finland ta ki biyan kudin cinikayyar da kudin rubles na Rasha kamar yadda aka bukata.

    Amma hakan na da alaka da matakinta na komawa mamba a Neto.

  10. Ana gudanar da bincike kan gawar da aka tsinta a filin jirgin sama a Legas

    Getty Images

    Hukumomin filin jirgin sama a Najeriya suna binciken bayan tsintar wata gawar mutum a filin jirgin sama na Legas.

    Gawar da ba a gano ko ta wacece ba an bayyana samunta ne a safiyar ranar Alhamis, bayan wata sanarwa da hukumomin filin jirgin sama suka fitar da sanarwa kan lamarin.

    An rufe filin jirgin na kimanin sa a biyu da rabi domin bayar da damar dauke gawar, in ji sanarwar.

  11. Taliban ta kori wata 'yar jarida daga dakin taro a Herat

    bv

    Rahotanni daga Herat na cewa jami'an Taliban sun kori Marjan Wafa wata 'yar jaridar gidan radiyo Kilid daga wani taron manema labarai jiya Alhamis.

    A cewar rahotannin Naima al-Haq Haqqani, daraktan yada labarai da al'adu a Herat ce ta sa aka kori Wafa daga zauren.

    A baya-bayan nan Taliban ta kara sanya wa mata 'yan jarida takunkumi. A wata sabuwar dokar da ta sanya a bayan nan itace dole kowacce mace 'yar jarida mai gabatar da shiri a talabijin ta rika rufe fuskarta.

    A watanni farko da Talaiban ta kwace mulki, ba ta damu da harkokin mata da ke aiki a gidajen watsa labarai ba masu zaman kansu, amma a yanzu dokokinsu sun shafi kowacce yar jarida a hannu.

  12. Wacce rawa Gerrard zai iya takawa a wasansa da Man City don taimakawa Liverpool?

    >

    Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce tsohon dan wasan kungiyar kuma kocin Aston Villa Steven Gerrard zai dauki wasan da zai buga da Manchester City da mahimmanci.

    Liverpool na biye wa City da maki guda a gasar, yayin da ya zama saura wasa guda a kare wannan kakar.

    Gerrad zai iya taimakawa tsohuwar kungiyarsa ta ci Premier na bana, idan ya doke City ko kuma suka yi canjiras ita kuma Liverpool ta doke Wolves.

    "Zan iya fahimtar wannan yanayin idan na sa kaina a matsayin Gerrard," in ji Klopp.

    "Idan zai iya wasan da zai taimakawa tsohuwar kungiyata Borussia Dortmund or Mainz, kenan nima akwai wanda zai iya taimako na wani lokacin.

    "Sai dai bana buga wasa da kafata haka shi ma Stevie. Babu dadi ba na bugawa shi ma ba ya bugawa."

  13. Za mu gabatar da Magu gaban kotu nan gaba - Ministan 'yansanda

    .

    Ministan harkokin 'yan sanda, Mohammed Maigari Dingyadi, ya ce mukaddashin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu zai gurfana gaban kotu ne kawai idan an kawo rahoton binciken da ake gudanarwa a kan shi da mai shari'a Justice Ayo Salami-led ke jagoranta.

    Ya bayyana haka ne a jiya ya yin taron ministoci na mako-mako wanda tawagar 'yada labarai na shugabancin Najeriya a Abuja.

    A watan Yulin 2020, shugaba Muhammadu Buhari ya kafa wata tawaga da za ta gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa Magu, biyo bayan koken da Antoni Janar na kasa ya shigar Abubakar Malami.

  14. Japan za ta biya malaman makaranta a Afghanistan albashin wata biyu

    Nh

    Wakilin Japan a Afghanistan Takashi Okadar ya ce kasarsa za ta sake bude ofishin jakadancinta a Kabul kuma za ta karasa wasu ayyukanta da ba ta kammala ba.

    Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da mataimakin ministan cikin gida na Taliban.

    Ya kuma ce kasarsa za ta biya malaman makaranta albashin watanni biyu.

    Akwai malaman makaranta 290,000 a yanzu, ciki har da mata malamai 95,000 da ke aiki da gwamnatin Taliban.

    Tun da farko, jami'ai daga UNICEF sun sanarda kaddamar da wani shiri na biyan malaman makaranta kai tsaye.

  15. Kawo yanzu 'yan Boko Haram 53,262 ne suka mika wuya - Hedikwatar tsaro

    .

    Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce ya zuwa ranar 16 ga watan Mayu mayakan Boko Haram 53,262 ne suka mika wuya ga hukumomi.

    Ta ce mambobin kungiyar 1,627 sun mika wuya tare da iyalansu, ciki har da maza 331 da mata 441 da yara 855 sun mika wuya ga sojoji a yankuna daban-daban tsakanin 1 ga watan Mayu da kuma 14 ga watan.

    Daraktan Hedikwatar ta bangaren watsa labarai, Manjo Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana hakan a Abuja.

    Ya ce dakarun Najeriya na rundunar hadin kai sun kashe 'yan ta'adda 43, tare da kama 20 da kuma ceto mutum 63 cikin wadanda aka kama a fadin arewa maso gabahsin kasar cikin mako uku.

    Ya ce sun kashe kwamandan Boko Haram Abubakar Sarki a dajin Sambisa a Yuwe da ke karamar hukumar Koduga a jihar Borno.

  16. Biden zai kai ziyara Koriya Ta Kudu

    Getty Images

    Nan ba da jimawa ba Shugaba Biden zai isa Koriya ta Kudu a ziyararsa ta farko a Asiya a matsayin shugaban kasa.

    Damuwa game da muradin nukiliyar Koriya ta Arewa na iya zama kan gaba a ajandar taron.

    Pyongyang ta yi watsi da kiran dakatar da shirin samar da makamin nukilya, kuma ana fargabar cewa za ta iya yin gwajin makamin yayin ko kuma bayan ziyarar ta Mista Biden.

    Ana kuma kallon ziyarar ta Biden a matsayin wani kokarin aikawa China sakon cewa duk da yakin da ake yi a Ukraine, Amurka ba ta manta da kawayenta Na Asiya ba.

  17. Najeriya na bukatar shugaban da zai yi babu sani babu sabo - Obasanjo

    .

    Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce Najeriya na bukatar shugabanni masu ɗan taɓin hankali da za su iya mai da kasar kan turba mai dorewa.

    Obasanjo ya bayyana haka lokacin da ya karbi bakuncin dan takarar shugaban Najeriya karkashin jam'iyyar PDP, Mohammed Hayatu-Deen a Abeokuta, a gidansa da ke Ogun inda gidansa yake.

    Ya nuna bacin ransa kan halin da Najeriya ke ciki ba wai kawai koma bayan ba ne gare shi, da kuma wadanda suka damu da Najeriya baki daya.

    Tsohon shugaban ya jaddada cewa, Najeriya za ta iya kawo karshen matsalar tsaron da take fama da ita cikin shekara biyu in ta samu shugaban da ya dace wanda kuma yake fatan daukar matakan da suka dace.

  18. An kashe sojojin Burkina Faso 11 a wani sansaninsu

    .

    Rundunar sojin Burkina Faso ta ce an kashe sojinta 11 yayin wani hari da aka kai musu sansaninsu na Madioari a gabashin kasar a ranar Alhamis.

    A kalla kuma an jikkata wasu 20 na daban amma dukansu suna karbar magani kamar yadda sashen yada labarai na rundunar ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.

    Babu dai wata kungiyar da ta dauki alhakin kai wannan hari ya zuwa yanzu.

    Rundunar ta ce sojijinta na sama sun kashe akalla 'yan bindiga 15 wadanda suke kokarin tserewa bayan kai harin.

    Burkina Faso na fama da masu ikirarin jihadi a yankin arewacin kasar tun 2015.

  19. Rasha ta lalata yankin Donbas baki daya - Zelensky

    BBC

    Shugaba Volodymyr Zelensky ya ce sojojin Rasha sun lalata yankin gabashin Donbas da ke Ukraine gaba daya.

    A cikin jawabinsa na bidiyo na dare, Mista Zelensky ya bayyana halin da ake ciki a Donbas a matsayin mummuna, yana mai zargin Rasha da kai hare-haren bama-bamai.

    A jawabin na kullu yaumin ya kuma kara da cewa Ukraine na ci gaba da kwato wasu birane a kusa da Kharkiv.

    Rasha dai ta mayar da hankali kan yankin Donbas, wanda ya kunshi lardunan Donetsk da Luhansk inda 'yan awaren da ke samun goyon bayan Moscow suka kwashe shekaru suna fafatawa da sojojin Ukraine.

  20. Mutum hudu sun nutse, 10 sun bata a tekun Tunisia

    BBC

    Akalla mutum hudu ne suka nutse a teku wasu 10 na daban suka yi batan dabo, yayin da jirginsu ya nutse a gabar tekun Tunisia.

    Masu gadin tekun sun ce mutanen 'yan ci-rani ne da ke kokarin tsallaka bahar rum su shiga Italiya.

    Masu gadin tekun sun ceto mutum 44 daga jirgin da aka cika da mutane sama da yadda ya kama.

News Navigation

Comments