YADDA MUTANAN AFRICAN SUKE HAKKO GOLL ACIKIN KARKASHIN KASA 2022 #LABARINHAUSA00 TAKUCI

Abin da ya sa 'yan Gambiya suke kaɗa ƙuri'a da duwatsu

A voter in Gambia holding up a marble used to vote - archive shot

ASALIN HOTON,AFP

A jerin wasikun da 'yan jaridar Afirka ke aiko mana, marubuci dan Saliyo da Gambia, Ade Daramy ya ce cikin shekaru biyar 'yan Gambia sun ga sauyin siyasa iri daban-daban, sai dai salon yadda suke kada kuri'ar zaben shugabanni bai sauya ba ko kadan.

Yawancin 'yan kasar na alfahari da salon yadda suke kaɗa ƙuri'a da ya bambanta da na sauran ƙasashe.

Idan suka je rumfunan zaɓe a ranar 4 ga watan nan, domin zaɓar shugaban kasa ba za a yi amfani da takardun kaɗa ƙuri'ar ba.

Maimakon hakan, da zarar sun isa rumfar zaɓe, bayan an kammala tantance su, za a nuna wa mai kaɗa ƙuri'a wani duro da aka yi wa fenti da alamar jam'iyyun siyasar ƙasar da ƴan takara.

Saman duro ɗin a rufe yake ruf, sai wani ƙaramin bututu da aka sa a sama, inda a nan jami'an hukumar zaɓe za su bai wa kowanne mai kaɗa ƙuri'a wani farin dutse mai garai-garai da zai jefa ta bututun da ke sama ga dan takarar da yake son zaɓa.

GAME BUQATAN WASU KARIN BAYANIN GAME DA QATAN MU SHAFIN MU NA FACEBOOK 

FACEBOOK
INSTAGRAM
YOUTUBE
AND OTHERS


Comments