BBC News, Hausa
Tsallaka zuwa abubuwan da ke ciki
Sassa
Labaran DuniyaWasanniNishadiCikakkun RahotanniBidiyoShirye-shirye na MusammanShirye-shiryen rediyo
TALLA
Osinbajo zai kaddamar da takarar shugabancin Najeriya
Mintuna 32 da suka wuce
Farfesa Yemi Osinbajo
A ranar Litinin din nan ne mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, zai bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.
A cewar wasu majiyoyi na shirin kaddamar da takarar sun ce ba wani taro na musamman za a yi wajen kaddamar da takarar ba.
Illa kawai za a fitar da wani hoton bidiyo wanda zai yi jawabi a kan burinsa na gadar Shugaba Muhammadu Buhari.
Za a sanya bidiyon a dukkan kafofin intanet, daga nan kuma sai 'yan kwamitin yakin neman zabensa su fara yakin gadan-gadan.
TALLA
Prof Yemi Osinbajo: Buhari ne ɗan siyasar Najeriya mafi shahara
Bola Tinubu: Tsohon gwamnan Legas ya shaida wa Buhari zai yi takarar shugaban ƙasa a 2023
Dokar zaɓen Najeriya: Mece ce makomar ministocin Buhari da ke son tsayawa takara?
Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya gabatar da jawabi ga wani taron jama'a inda ya kaddamar da manufarsa ta tsayawa takara kamar yadda tsohon gwamnan jihar Rivers, kuma ministan sufuri Rotimi Amaechi ya yi a Fatakwal a ranar Alhamis din da ta wuce.
Shi kuwa tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan Ebonyi David Umahi, su sun yi bayani ne ga 'yan jarida a lokacin kaddamar da takarar tasu, bayan sun gana daban-daban da Shugaba Buhari.
Rahotanni sun ce kafin sakin bidiyon da za a yi a ranar Litinin, sai da Mr Osinbajo, ya yi buda baki tare da gwamnonin jam'iyyar APC a gidansa.
Tuni dai Osinbajo ya bude ofishin kamfen dinsa a Wuse da ke Abuja.
Baya ga kewayawa da zai yi jihohi domin neman goyan baya, 'yan kwamitin yakin neman zaben nasa za su shirya kuri'ar jin ra'ayin jama'a domin tattara shawarwari game da matakin da ya dauka na tsayawa takarar a zaben 2023.
A daya daga cikin tambayoyin da ke cikin wannan kuri'a ta jin ra'ayi, an tambayi jama'a kan su zabi wanda suka ga ya fi dacewa da shugaban kasa tsakanin tsohon gwamnan jihar Kano Rabi'u Musa Kwankwaso da Tinubu da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.
Ana ganin Farfesa Osinbajo, zai samu magoya baya, amma yadda zai bullo a siyasance ya kalubalanci manyan masu sha'awar takarar biyu Mr Tinubu da Mr Amaechi, shi ne abin jira a gani.
Labarai masu alaka
Najeriya
Zaben shugaban Najeriya na 2023
Siyasar Najeriya
Babban Labari
Ukraine za ta gamu da matsalar tattalin arziki - Bankin Duniya
Mintuna 38 da suka wuce
RB Leipzig za ta yi wa Manchester Utd yankan baya, PSG na son Lukaku
Mintuna 37 da suka wuce
Osinbajo zai kaddamar da takarar shugabancin Najeriya
Mintuna 32 da suka wuce
Minti Daya Da BBC
1:08
Saurari, Minti Daya Da BBC Na Rana 08/04/2022, Tsawon lokaci 1,08
8 Aprilu 2022
Korona: Ina Mafita?
Wanda aka fi karantawa
1
RB Leipzig za ta yi wa Manchester Utd yankan baya, PSG na son Lukaku
2
Osinbajo zai kaddamar da takarar shugabancin Najeriya
3
Wane ne ɗan Daudu, kuma me ake ɗaukar sa a ƙasar Hausa?
4
Waiwaye: Za a kashe tiriliyan huɗu a biyan tallafin mai, an cire dokar hana taron biki a Najeriya
5
Ukraine za ta gamu da matsalar tattalin arziki - Bankin Duniya
BBC News, Hausa
Me ya sa za ku iya aminta da BBC
Sharuddan yin amfani
A game da BBC
Ka'idojin tsare sirri
Ka'idoji
Tuntubi BBC
AdChoices / Do Not Sell My Info
© 2022 BBC. BBC ba za ta dauki alhakin abubuwan da wasu shafukan daban suka wallafa ba. Karanta hanyoyin da muke bi dangane da adireshin waje.
Gaskiya mungode
ReplyDeleteMasha allah
ReplyDelete