Wata kotu a birnin Lubumbashi a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ta samu dukkan mutum 10 da ake tuhuma da laifuka uku ciki har da yin fyade ga wasu mata fursunoni lokacin wata tarzoma da laifi.Sauran laifukan da aka same su da
Wata kotu a birnin Lubumbashi a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ta samu dukkan mutum 10 da ake tuhuma da laifuka uku ciki har da yin fyade ga wasu mata fursunoni lokacin wata tarzoma da laifi.
Sauran laifukan da aka same su da aikata su ne yunkurin tserewa daga gidan kaso, da cinna wuta a gidan yari a lokacin tarzomar da aka yi a gidan yarin Kasapa mai matukar tsaro, a shekarar 2020.
Kotun ta umarci biyan diyyar $50,000 ga mutum 19 da suka kai kara gabanta, kudin da bai kai abin da lauyoyinsu suka bukaci a biya ba wato $1m.
An kwashe watanni biyu ana gudanar da shari'ar kafin a yanke hukunci a yau, amma sai da wadanda suka kai karar suka kwashe sama da shekara daya kafin a gabatar da wadanda ake zargi a gaban kotu.
'Yan bindiga sun harbe shugabannin APC a Enugu
Copyright: OTHERWasu 'yan bindiga sun yi kutse a wajen wani taron shugabannin jam'iyyar APC a karamar hukumar Enugu ta kudu inda suka bude musu wuta a ranar Talata.
Rahotanni sun ce 'yan bindigar kusan bakwai sun kashe mutum biyu suka raunata wasu da dama yayin da suka yi awon gaba da mutum daya daga cikin shugabannin na APC na mazaba ta uku ta unguwar Obeagu Awkunanaw a karamar hukumar ta Enugu ta kudu.
Daya daga cikin wadanda 'yan bindigar suka kashe shi ne, tsohon shugaban jam'iyyar na karamar hukumar na baya-bayan nan, wanda kuma shi ne mataimakin shugaban matasa na jan'iyyar na jihar a yanzu, Mista Kelvin Ezeoha.
Rahotanni sun ce ba a san ko harin na da nasaba da siyasa ba ko kuma hari ne na haramtacciyar kungiyar 'yan aware ta Biyafara ba, IPOB, wadanda suke kai hare-hare a kan jama'a a yankin kudu maso gabas na Najeriya da sunan tabbatar da dokar zama a gida.
Zuwa lokacin hada wannan rahoto rundunar 'yan sanda ta jihar ta Enugu ba ta ce komai ba ko fitar da wata sanarwa dangane da harin.
Mali na zawarcin makwabta domin kewaye wa takunkumin Ecowas
Copyright: AFPImage caption: 'Yan Mali sun yi zanga-zangar kin amincewa da takunkumin Ecowas a kan kasarsu a makon da ya gabata Hukumomin soji na Mali sun shiga zawarcin makwabtan kasashe, Guinea da Mauritania a kokarin da suke na kewaye wa takunkumin da kungiyar Ecowas ta sanya wa kasar.
Ecowas ta sanar da matakin sanya wa kasar takunkumin ne bayan da gwamnatin sojin kasar ta sanar da dage zaben da a da ta ce za ta yi a watan Fabrairu, har zuwa shekara hudu, bayan juyin mulkin da suka yi a watan Agusta na 2020 da kuma Mayu na 2021.
Takunkumin ya hada da rufe iyakokin katafariyar kasar ta Yammacin Afirka da kuma na kasuwanci.
Hukumomin na Mali na neman hadin kan Guinea kasancewar ita ma an dakatar da ita daga kungiyar ta Ecowas bayan juyin mulkin da soji suka yi a watan Satumba da ya wuce, yayin da ita kuma Mauritania ba ta cikin kungiyar Ecowas.
Wata babbar tawaga daga Malin ta je Conakry ranar Litinin, yayin da wata tawagar ta daban kuma ta nufi Nouakchott ranar Talata domin tattauna hanyoyin da za su bi domin saukaka tafiye-tafiyen mutane da safarar kaya.
Bayan Guinea da Mauritania, Mali tana da iyaka da Algeria da Burkina Faso da Niger da Ivory Coast da kuma Senegal.
An sauke Ministan Shari'ar Sierra Leone
Copyright: Sierra Leone Attorney General's OfficeImage caption: An nada Anthony Yeiwoh Brewah a kan mukamin a 2020 Shugaban Saliyo Julius Maada Bio ya sauke babban lauyan gwamnati kuma Ministan Shari'ar kasar, wato antoni janar daga mukaminsa.
Ba wani dalili da fadar shugaban kasar ta bayar kan dalilin sauke Anthony Yeiwoh Brewah daga aiki.
Sai dai kafofin yada labarai na kasar na danganta cirewar ga afuwar da aka yi wa fursunoni a ranar sabuwar shekara da kuma wani hoto da aka gani ministan ya dauka da wani daga cikin 'yan kason da aka saki.
Kafofin yada labarai na kasar sun ruwaito cewa Mista Brewah yana cikin kwamitin da ya ba wa shugaban kasar shawarar yafe wa 'yan sarka 160.
Bayan an saki fursunonin ne kuma aka ga antoni janar din a wani hoto da ya dauka a gidansa tare da daya daga cikin fusunonin da aka saki Baimba Moi Foray, wanda aka yanke wa hukunci kan laifin kisan wani mai sanya kade-kade, abin da ya janyo bacin ran jama'a.
Tuni aka soke yafiyar da aka yi wa Foray.
Tsohon ministan bai ce komai ba a kan hoton da kuma cire shi daga mukamin.
Yanzu an maye gurbinsa da Mohamed Lamin Tarawalley.
An bai wa gwamnatin Buhari shawarar kara farashin fetur zuwa N302
Copyright: OtherImage caption: Kara farashin mai a Najeriya kan janyo hauhawar farashin kayayyaki da ayyuka a kasar Watakila gwamnatin Najeriya ta kara farashin man fetur zuwa naira 302 a kan kowa ce lita a wata mai zuwa, Fabrairu, kamar yadda majalisar kasa kan tattalin arziki ta bayar da shawara a watan Nuwamba na 2021, kamar yadda jaridar TheCable ta labarto.
Jaridar ta ruwaito cewa tana ganin wannan na daga cikin shirin gwamnati na janye hannunta kacokan daga harkar sanya farashin man, domin kawo karshen tallafin da take biya a kowane wata, ta yadda kasuwa za ta yi halinta a samu gogayya kan farashin.
A yanzu dai ana sayar da man fetur a yawancin sassan Najeriya a tsakanin naira 162 da 165 a kan kowace lita.
Kwamitin wucin-gadi na majalisar kula da tattalin arziki wanda ya tattauna da kamfanin mai na kasar (NNPC) a kan farashin da ya dace a sa shi ne ya bayar da shawarar kara kudin ta hanyar janye tallafin.
Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai, wanda shi ne shugaban kwamitin, shi ya gabatar da rahoton.
Ghana ta musanta shirin karbar masu neman mafaka na Birtaniya
Gwamnatin Ghana ta musanta cewa tana duba yuwuwar kafa cibiyar karbar masu neman mafaka na Birtaniya.
Kafofin yada labarai da yawa na Birtaniya sun ruwaito cewa Birtaniya na tsara yadda za ta tura dubban masu neman mafaka zuwa kasashe irin su Ghana da Rwanda domin tsugunar da su a can karkashin wani shiri da aka yi wa lakabi da Ingilishi "Operation Dead Meat", wanda ke nufin kamar kawar da ''Mushe''
A wani sakon tuwita ma'ikatar harkokin waje ta Ghana ta ce ba ta yi wata tattaunawa da Birtaniya ba a kan batun kuma ba ta da niyyar yin wani abu kamar haka a nan gaba.
A shekarar da ta gabata Rwanda ta ce duk da cewa ta kulla yarjejeniyar karbar masu neman mafaka da kasar Denmark, ba ta cikin wannan shiri na Birtaniya.
A shekarar da ta wuce kungiyar tarayyar Afirka ta nuna kin yardarta da shirin mayar da masu neman afuwa daga Turai zuwa Afirka, tana mai cewa shiri ne na kyama wanda ba za a amince da shi ba sam.
Chadi ta fara sakin 'yan tawaye 250 kafin tattaunawar zaman lafiya
Copyright: AFPImage caption: Hukumomin Chadi sun yi alkawarin sakin fursunoni 'yan tawaye da ke tsare karkashin shirin afuwa Hukumomin gwamnatin rikon-kwarya a Chadi sun saki wasu fursunoni 'yan tawaye daga cikin 250 da suke tsare da su, kamar yadda suka yi alkawari a karkashin wani shirin afuwa.
Ministan Tsaro na kasar Ahmat Mahamat Alhabo shi ne ya jagoranci sakin fursunoni 22 da aka kama da laifin daukar makamai su yaki kasar, a yayin wani kwarya-kwaryan biki da aka yi a wani gidan yari da ke kusa da babban birnin kasar.
An gayyaci kungiyoyin 'yan tawaye da su shiga tattaunawar maido da zaman lafiya a kasar ta Yammacin Afirka, da za a fara a wata mai zuwa.
Daya daga cikin wadanda aka yi wa afuwar Samedi Torde Tanel, ya gode wa wadanda suka yi uwa suka yi makarbiya aka sake su, tare da yin fatan sauran abokan gwagwarmayarsu ma za su ci moriyar wannan afuwa.
An bullo da shirin afuwar da sasantawa ne bayan mutuwar Shugaba Idriss Déby a fagen daga a watan Afrilu na shekarar da ta wuce.
Hukumar rikon-kwarya da ke mulkin kasar ta Chadi a yanzu na karkashin jagorancin dan marigayin ne Mahamat Idriss Déby.
Abacha ya yaudari 'yan siyasa - IBB
Copyright: OTHERTsohon shugaban mulkin sojin Najeriya Sani Abacha, wanda ya mulki kasar daga 1993 har lokacin mutuwarsa a 1998, ya hau mulkin ne bayan ya yaudari ‘yan siyasa, a cewar Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Janar Babangida ya bayyana haka ne a hirarsa da Trust TV, yayin da yake bayyana yadda Abacha ya yi yaudari mutane ya kwace mulki.
Abacha, wanda IBB ya bayyana a matsayin “babban abokina”, ya kasance hafsan hafsoshin sojoji a lokacin mulkin Babangida daga 1985, kuma daga baya ya nada shi Ministan Tsaro a 1990.
Babangida ya ce, gwamnatin Abacha tana da wayo. Sun san wadanda suka fi magana a kan zabe da juyin mulkin da batun 12 ga watan Yuni da sauran abubuwa.
Sai suka fara magana da su, suka yaudare su da karfafa musu guiwa su kawar da gwamnatin rikon-kwarya, da cewar idan sun kawar da gwamnatin rikon-kwaryar, za su dawo da su, su ba su abin da suke so mulkin dumokuradiyya, daga nan sai a kafa gwamnatin farar hula.
Babangida ya ce: ''Da wannan suka yaudari jama'a da sauran fitattun mutane, saboda haka da Abacha ya shigo, sai ake ta murna, hankali ya kwanta; Madalla abu ya yi kyau! Abin da zai faru a gaba kuma shi ne zababbiyar gwamnatin dumokuradiyya. Ni na sani, mun sani, hakan ba zai yiwu ba saboda maganar ita ce: (Abacha zai ce ), Me zai sa in sa kaina cikin hadari, kawai in zo in danka muku mulki?' Wannan shi ne abin da ya faru.'' In ji Babangida.
Korona ta kashe karin mutum shida a Najeriya ranar Talata
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 163 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar ranar Talata 18 ga watan Janairun 2022.
Daga cikin sabbin wadanda suka kamu jihar Legas tana kan gaba inda take da mutum 59, sai babban birnin ƙasar Abuja mai 33, sai jihar Delta da ke kudu maso kudancin ƙasar, inda aka samu mutum 16.
A Kaduna kuwa an samu mutum 13 ne da suka kamu da cutar, yayin da aka samu 12 a jihar Gombe, baya ga ƙarin wasu mutane 12 da aka samu a jihar Osun.
Sauran jihohin da aka samu cutar su ne Ogun mai mutum 4, da Ekiti mai mutum 3, da Oyo mai mutum 3, da Rivers mai mutum 3, da Borno mai mutum 2, da Imo mai mutum 2, sai kuma jihar Nassarawa da aka samu mutum guda da ya kamu.
Barkanmu da warhaka
Muhammad Annur Muhammad ne ke yi muku maraba da kasancewa da ku a wannan shafin da muke kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.






Comments
Post a Comment