LABARIN HATSIN ABINCHIN YAN AREWA Amsar tambaya biyar kan dalar shinkafar da Shugaba Buhari ya kaddamar
Amsar tambaya biyar kan dalar shinkafar da Shugaba Buhari ya kaddamar
- Umar Mikail & Fauziyya Tukur
- BBC Abuja Bureau

A ranar Litinin ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yaye kallabin dalar buhunan shinkafa mafi girma da aka taɓa tattarawa a tarihin ƙasar domin nuna irin ci gaban da gwamnatinsa ta samu wajen noman shinkafa.
An tattara dala-dalar shinkafar 13 wadda aka yi miliyoyin buhunan shinkafa a dandalin baje-koli na babban birnin kasar a Abuja.
Ga amsar wasu tambayoyi da ƴan Najeriya ke ta yi wa kawunansu dangane da batun dalar shinkafar.
Mece ce gaskiyar hoton dalar katako da ake yaɗawa?
Wani hoto da aka dinga yaɗawa a shafukan zumunta ya nuna dalar shinkafa ɗauke da jerin katakwaye a tsakiya da nufin ita ce dalar da Shugaba Buhari na Najeriya ya ƙaddamar ranar Talata a ABuja.
An yi ta yaɗa hoton musamman a Facebook da WhatsApp da zimmar dakushe bikin ƙaddamar da dalar shinkafar da gwamnati ta ce ita ce mafi girma a duniya da aka taɓa yi.
Gwamnatin Buhari ta ce an tattara buhunan shinkafa fiye da miliyan ɗaya da aka karɓa daga manoma a faɗin jihohin ƙasar da suka samu tallafi ta cikin tsarin Anchor Borrower Programme na Babban Bankin Najeriya CBN.
Sai dai binciken da Sashen Bankaɗo Labaran Ƙarya na BBC ya gudanar ya gano cewa hoton ya fara ɓulla ne a dandalin Nairaland tun watan Janairun 2018, inda aka yi amfani da shi a wurare da dama.
Binciken ya gano cewa an ɗauki hoton ne yayin irin wannan bikin na dalar shinkafa a Jihar Ogun.
LabarinHausa00 TAKUCI
ZAKU ne memu. A social media
Comments
Post a Comment